Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
"Ba da ilmi ta yanar gizo" ya sa daliban karkara sun iya samun nagartaccen ilmi
2020-07-15 13:05:06        cri

Cikin 'yan shekarun nan, ta hanyar ba da ilmi ta yanar gizo, daliban karkarar lardin Hunan na kasar Sin sun sami karin ilmi mai nagarta. Yang Jinmin mai shekaru 13da haihuwa yana zama a kauyen Bilang na garin Xinhuang na lardin Hunan, wurin dake kewaya da tsaunuka, inda ake fama da karancin harkokin dake shafar ba da ilmi. Galibin mutanen kauyen sun fara aiki bayan sun gama karatun makarantar sakandare, kusan ba wanda ya iya shiga jami'a, da kuma fita daga kauyen.

Amma, wannan lamari ya canja bayan da aka kafa wata makaranta a kauyen, wadda ta kyautata harkokin ba da ilmi na wurin. Da nufin kyautata ayyukan ba da ilmi a wurare masu fama da talauci, lardin Hunan ya kafa wasu sabbin makarantun zamani domin karbar daliban da suka fito daga gidaje masu fama da talauci, inda aka sanya wa makarantun suna "Fu Rong".

A shekarar 2019, an fara karbar dalibai a makarantar Fu Rong na garin Xin Huang, sa'an nan, Yang Jinmin ya shiga wannan makaranta daga makarantar kauyensu. Azuzuwa guda 35 na makarantar sun kafa tsarin koyon ilmi ta yanar gizo da wasu shahararrun makarantun birane, ta yadda, za a ba da ilmi ga daliban makarantar Fu Tong ta yanar gizo bisa lokacin da aka tsara.

Yang Jinmin ya yi farin ciki kwarai bayan ya shiga wannan makaranta, karatunsa a fannin lissafi ya kyautata sosai.

Yanzu, gaba daya an kafa makarantun Fu Rong guda 16 a lardin Hunan, sa'an nan, ya zuwa shekarar 2021, za a kafa makarantun Fu Rong guda 100 a dukkanin garuruwa masu fama da talauci a lardin Hunan, sa'an nan, daliban yankin karkara kimanin dubu 150 za su sami nagartaccen ilmi a wadannan makarantu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China