Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bakauyen Da Ya Rubuta Bayanai Kan Yadda Ya Fita Daga Kangin Talauci
2020-07-13 16:20:23        cri
Wang Wancai mazaunin kauyen Wangzhuang dake karkarar gundumar Tanghe na lardin Henan, ya zama abin misali inda ya zama attajiri bayan fita daga kangin talauci.

Wang Wancai ya bar makaranta saboda rashin kudin jiyya bayan ya kamu da wata cuta. Bayan ya yi aure, dansa ya gamu da matsalar laka, kuma ba zai iya kula da kansa ba. Hakan ya sa Wang Wancai na sallamawa rayuwa duhu saboda halin da yake ciki na rashi

A shekarar 2016, mataimakiyar darektan kwamitin dake kula da gundumar Tanghe kai tsaye Guo Youxia ta fara taimakawa Wang Wancai. Daga waccan lokaci, Wang Wancai ya farfado da aikin gona, kuma ya shiga aikin sa kai a fannin kiwon lafiya da ake gudanarwa a kauyen. Ban da wannan kuma, dansa ya amfana da manufar tallafin jiyya na gwamnati. Yanzu haka, Wang Wancai ya fara bude wani shagon samar da abincin Doufu a harabar gidansa.

Tun rana ta farko da Guo Youxia ta taimakawa Wang Wancai, Wang Wancai ya rubuta gajeren bayani game da fita daga kangin talauci, kalmomin da ya rubutu sun wuce dubu 120. A cikin wannan littafi, ya rubuta yadda ya yi fama da talauci da kuma kuncin da ya shiga yana yarinta, da juriya, da kauna da yadda aka taimakawa masa wajen fito daga kangin talauci da farin cikin iyalansa bayan ya fita daga talauci har ya zama attajiri. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China