Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IIF:Tattalin arzikin Sin ya kara farfadowa bayan cutar COVID-19
2020-07-09 11:26:02        cri
Cibiyar bincike game da hada hadar kudade ta kasa da kasa ta IIF, ta ce tattalin arzikin kasar Sin ya yi kyakkyawar farfadowa, bayan komadar da ta biyo bayan bullar cutar COVID-19, da ma matakan da kasar ta aiwatar na shawo kan cutar.

Cikin wani rahoto da masanan cibiyar ta IIF suka fitar, sun ce tattalin arzikin Sin ya farfado cikin sauri, bayan babban koma baya da ya fuskanta. Kaza lika tattalin arzikin kasar na kara bunkasa cikin watanni 3 na biyun wannan shekara, sabanin yanayin da aka fuskanta a watanni 3 na farkon shekarar.

Rahoton ya kara da cewa, Sin na kan hanyar samun cikakkiyar farfadowa, yayin da masana'antu da kamfanonin sarrafa hajoji ke kara bude harkokin su bayan kalubale mai tsanani da suka gamu da shi, ko da yake fannin sayar da kayayyakin masarufi na ci gaba da fuskantar koma baya.

Duk da cewa fannin sayar da kayan masarufin na fuskantar kalubale mai wuyar sha'ani a yanzu, cibiyar IFF ta yi hasashen shawo kan wannan kalubale nan gaba cikin nasara.

Rahoton ya kara da cewa, bisa matakan da Sin ta aiwatar, ana iya gane cewa, cikakkiyar farfadowar sashen masana'antu za ta samu ne kawai a kasashen da suka aiwatar da ka'idojin shawo kan bazuwar COVID-19 yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China