Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi Allah wadai da harin da aka kaiwa jami'an wanzar da zaman lafiya a CAR
2020-07-15 10:20:58        cri
Kwamitin sulhun MDD ya yi Allah wadai da harin da aka kaddamar ranar Litinin kan jami'an shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake jamhuriyar tsakiyar Afrika CAR, inda wani jami'in wanzar da zaman lafiyar dan kasar Rwanda ya rasa ransa, kana wasu mutanen biyu sun samu raunuka.

A sanarwar da aka rabawa manema labarai, mambobin kwamitin sulhun MDDr sun bayyana ta'aziyya da jajantawa iyalan jami'in wanzar da zaman lafiyar da aka hallaka, kana sun jajantawa gwamnatin kasar Rwanda da tawagar wanzar da zaman lafiyar ta MINUSCA. Sannan sun yi fatan samun lafiya cikin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka a harin.

Mambobin kwamitin sulhun MDDr sun yi Allah wadai da babbar murya ga dukkan hare-haren, da neman tsokana, da duk wani cin zarafi da kungiyoyin masu dauke da makamai ke yiwa dakarun MINUSCA. Sun jaddada cewa, duk wani hari kan jami'an shirin wanzar da zaman lafiyar tamkar aikata laifukan yaki ne kana sun tunatar da dukkan bangarori game da kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansu karkashin dokokin kasa da kasa. Sun bukaci gwamnatin CAR da ta gaggauta bincike kan harin domin hukunta wadanda ke da hannu.

Mambobin kwamitin MDDr sun jaddada goyon bayansu ga shirin MINUSCA, kana sun bayyana gamsuwar bisa kokarin da MINUSCA ke yi da irin gudunmawar da kasashen duniya ke bayarwa wajen samar da jami'an 'yan sandan kiyaye zaman lafiyar.

A ranar Litinin ne aka kaddamar da harin kan ayarin jami'an tsaron MINUSCA a yankin Gedze dake shiyyar arewa maso yammacin lardin Nana-Mambere. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China