Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata tawagogin wanzar da zaman lafiya su taimakawa kasashe wajen magance COVID-19
2020-07-08 10:16:25        cri

Wakilin dindindin a MDD Zhang Jun, ya ce kamata ya yi tawagogin MDD masu aikin wanzar da zaman lafiya, su tallafawa kasashen da suke aiki a cikin su, wajen shawo kan cutar numfashi ta COVID-19, tare da tabbatar da cewa, al'ummun kasashen sun samu kariya ga rayuka da lafiyar su.

Zhang Jun, wanda ya bayyana hakan yayin taron da kwamitin tsaron MMDr ya shirya, game da ayyukan wanzar da zaman lafiya da kare hakkin bil Adama, ya kara da cewa, al'ummun kasashen da ake gudanar da ayyukan wanzar da zaman lafiya na cikin mummunan yanayi ta fuskar kiwon lafiya.

Wadannan kasashe a cewarsa, sun hada da Sudan ta kudu, da Mali, da jamhuriyar dimokaradiyyar Congo. Ya ce matakan kare hakkokin bil Adama na da muhimmancin gaske, amma ana iya cimma nasarar aiwatar da su ne kawai, idan har akwai zaman lafiya da daidaito.

Daga nan sai ya jinjinawa ayyukan wanzar da zaman lafiya da MDDr ke aiwatarwa a sassan duniya daban daban, yana mai cewa, a matsayinsu na kyawawan kudurori da kwamitin tsaron MDD ke amfani da su wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro, ayyukan sun taka rawar gani wajen bunkasa yanayin zaman lafiya da lumana tsakanin al'ummun wadannan kasashe, tare da samar da damar bunkasuwa, da kare hakkokin al'ummun su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China