Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Guterres ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa jami'an MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a CAR
2020-07-14 09:46:28        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin da aka kaiwa jami'n majalisar dake aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya jiya Litinin, harin da ya sabbaba kisan ma'aikacin wanzar da zaman lafya dan kasar Rwanda kana wasu biyu suka jikkata.

Wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, Mr Guterres ya mika sakon ta'aziya ga iyalan mamatan gami da gwamnati da al'ummar Rwanda, tare da fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka jikkata.

Jami'in na MDD ya ce, hare-hare kan jami'an MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya, na iya zama laifukan yaki karkashin dokoki na kasa da kasa. Don haka ya yi kira ga hukumomin CAR da su farauto wadanda suka aikata wannan danyen aiki, don ganin sun girki abin da suka shuka.

Sanarwar ta kuma ruwaito Guterres na sake jaddada cewa, MDD za ta ci gaba da goyon bayan matakan da kasar ke dauka na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a CAR. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China