Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakataren MDD ya bayyana goyon bayansa kan matakan Sin na yaki ambaliyar ruwa
2020-07-14 09:49:52        cri

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres a jiya Litinin, ya bayyana goyon bayansa kan matakan da mahukuntan kasar Sin suke dauka kan yaki da ambaliyar ruwa.

Jami'in na MDD ya kuma mika wani sako ga zaunannen wakilin kasar Sin dake MDDr Zhang Jun, inda a cikinsa yake nuna goyon baya da ma jajantawa iyalan wadanda ambaliyar ruwa ta yiwa barna, gami da gwamnati da daukacin al'ummar Sinawa, sakamakon hasarar rayuwa da lalata wasu kayayyaki da ambaliyar ruwar ta haddasa a sassan kasar. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China