Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bayyana kudurinta na taimakawa aikin sauya fasalin bangaren tsaron Libya
2020-07-13 10:34:09        cri

Mai rikon mukamin wakilin sakatare Janar MDD a Libya, Stephanie Williams, ta bayyana kudurin majalisar na taimakawa hukumomin Libya dangane da sauya fasalin bangaren tsaron kasar.

Wata sanarwa da kungiyar wanzar da zaman lafiya na MDD dake aiki a Libya UNSMIL ta fitar, ta ce Stephanie Williams ta bayyana haka ne yayin wani taro ta kafar bidiyo da ya gudana ranar Asabar, tsakanin jami'an UNSMIL da na ma'aikatar harkokin cikin gida ta gwamnatin kasar Libya dake samun goyon bayan MDD.

Wakilan sun amince da dawo da shirye-shirye da wasu ayyukan da suka tsaya biyo bayan barkewar rikici a watan Afrilun 2019. Sun kuma jaddada alakar dake tsakanin sauya fasalin bangaren tsaro da na tattalin arziki.

Tun bayan hambarar da gwamnatin Gaddafi a 2011, Libya ke fama da karuwar rikice-rikice, ciki har da na siyasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China