Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kotun kolin Amurka ta amince da bukatar bada damar binciken bayanan kudaden shugaban kasar Trump
2020-07-10 10:37:05        cri
Kotun kolin Amurka a ranar Alhamis ta amince da bukatar da majalisar wakilan da jam'iyyar Demokarat ke da rinjaye ta nema game da batun bincikar bayanan kudin shugaban kasar Donald Trump, a yanzu kotun ta bada izini ga masu gabatar da kara a Manhattan da su binciki bayanan kudin shugaban.

Kotun kolin, a hukuncin shari'a mai lamba 7-2 wanda ta zartar, ta amince cewa Trump ba shi da ikon hana bincike da ya shafi bayanan harkokin kudinsa daga babban mai shari'a na gundumar Manhattan, Cyrus Vance, kasancewar shugaban kasar ba shi da wata dokar kariyar da ta hana a bincike shi.

Haka zalika, kotun ta ki amincewa ta gabatar da hukuncin karshe game da kwamitin majalisar wanda zai iya samun damar binciken bayanan kudin shugaban Trump, ta mayar da batun zuwa ga kananan kotuna.

Shi dai wannan hukunci yana nufin bayanan harkokin kudade na shugaban kasar Amurkar, wanda ya kunshi batun biyan kudaden harajinsa, mai yiwuwa ne a iya bincikarsa har zuwa bayan babban zaben kasar a watan Nuwamba, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bada rahoto. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China