Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bambancin da Amurka ke nunawa makaurata ya nuna munafuncinta a fannin hakkin dan Adam
2020-07-09 13:46:09        cri

Yau Alhamis, kungiyar nazarin harkokin hakkin dan Adam ta kasar Sin, ta fidda wani sharhi mai taken "bambancin ra'ayin da kasar Amurka ke nunawa makaurata, ya nuna munafuncinta a fannin hakkin dan Adam".

Cikin sharhin, kungiyar ta bayyana karuwar nuna wariya da kasar Amurka ke nuna wa makaurata ta fuskokin addinai, da al'adu da kuma launin fata da sauransu.

Sharhin ya ce kasar Amurka, tana matsa wa sauran kabilu lamba, ta hanyar tsara manufofin nuna bambanci, lamarin da ya keta 'yanci, da mutuncinsu, shi ya ma nuna wa kasa da kasa manufar munafunci ta kare hakkin dan Adam mai salon Amurka.

Haka kuma, sharhin ya nuna yadda gwamnatin kasar Amurka ke daidaita harkokin 'yan ci rani da karfin tuwo a yakunan iyakokinta. Har ta raba yara da mahaifansu, lamarin da ya keta ikon zaman rayuwa, da ikon kiwon lafiya nasu.

Cikin wannan sharhi dai, an bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin, Amurka ta kan nuna bambanci ga 'yan ci rani, sakamakon kiyayyar ta gare su, tana kuma gyara manufofin da abin ya shafa, ta yadda za su dace da bukatun Amurka. (Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China