Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za A Ga Sakamakon Yakar Cutar COVID-19 A Birnin Beijing A Kwanaki Biyu Ko Uku Masu Zuwa
2020-06-16 13:11:54        cri

A cikin kwanaki 5 da suka gabata, yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a birnin Beijing ya kai 106. A daren ranar 15 ga wannan wata, an yi hira da babban masani kan kula da magance cututtuka masu yaduwa na cibiyar magance cututtuwa ta kasar Sin Wu Zunyou game da yanayin hana yaduwar cutar a birnin Beijing.

Wu Zunyou ya bayyana cewa, bisa yanayin hana yaduwar cutar a dukkan kasar Sin, an samu wadanda suka kamu da cutar da dama ba zato ba tsammani a birnin Beijing, an shaida cewa, ana fuskantar yanayi mai tsanani. Amma likitoci sun gano kashi 6 cikin 10 a cikinsu kai tsaye. hakan ya shaida cewa, an gano abkuwar cutar cikin lokaci, da magance yaduwarta a fadin wuraren birnin. Yanzu ana kiyaye yanayin hana yaduwar cutar yadda ya kamata a birnin Beijing.

Yawan mutanen da za su kamu da cutar COVID-19 a kwanaki uku masu zuwa a Beijing zai shaida yanayin yaduwar cutar a birnin. Domin bayan da aka gano cutar a ranar 11 ga wata a Beijing, an dauki matakai nan da nan. Game da wadanda suka kamu da kwayoyin cutar, idan cutar ta fito, alamu za su fito a kwanaki biyu masu zuwa watoa wajen ranar 16 da 17 ga wata. Idan ba a kara samun yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar a kwanakin biyu masu zuwa ba, za a iya cewa yawan mutanen da suka kamu da cuatr ba zai karu sosai ba. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China