Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yarda da wallafa littafin da John Robert Bolton ya rubuta mai taken Labaran White House
2020-06-22 11:18:10        cri

 

Ran 20 ga wata agogon Amurka, alkalin tarayyar Amurka Royce Lamberth ya yarda da tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaron Amurka John Robert Bolton ya wallafa sabon littafin da ya rubuta mai taken "The Room Where It Happened: A White House Memoir". Shugaban kasar Donald Trump ya ba da sako a kan Twitter bayan ya samu sakamakon kotun, inda ya ce, Bolton ya sabawa doka, kuma zai dandana kudarsa. A cewarsa, shi kansa ya girbi abun da ya shuka.

An ce, gwamnatin Donald Trump ta kai kara gaban kotun yankin musamman na Washington a ran 16 ga wata, inda ta nuna cewa, sabon littafin da Bolton ya rubuta na kushe da sirri, idan aka gabatar da su a fili, za su illata tsaron kasar. A ran 17 ga wata, hukumar shari'a ta sake matsin lamba kan kotun da kuma yunkurin ba da umurni cikin gaggawa don hana wallafa wannan littafi.

Amma, kotun ba ta karbi bukatun gwamnatin Donald Trump ba. Mai kula da wannan batu alkali Royce Lamberth ya ce, ko da yake, matakin Bolton na wallafa sabon littafi ba tare da samun izni daga hukumar leken asiri ta kasar ba, ya kawo barazana ga kasar, amma babu wani sirri a cikin littafinsa.(Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China