![]() |
|
2020-07-08 10:25:28 cri |
Sanata Menendez, wanda memba ne a kwamitin huldar kasashen waje, ya ce matakan Trump na yaki da cutar numfashi ta COVID na cike da rudani da rashin tsari, wanda hakan ba zai taimaka wajen kare rayukan Amurkawa, ko muradunsu ba. Ya ce matakan na Trump sun bar Amurkawa yashe, cikin yanayi na rashin lafiya.
A wani ci gaban kuma, kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce babban magatakardar majalissar Antonio Guterres, ya karbi sakon da gwamnatin Amurka ta aike masa, game da aniyar janyewar Amurkan daga WHO.
Amurka ta kasance memba a WHO, tun daga ranar 21 ga watan Yuni na shekarar 1948, bayan da babban taron hukumar ya amince da shigarta, bisa kuma wasu sharudda na ficewa da ita Amurkar ta gindaya.
Sharuddan dai sun hada da sanar da WHOn shirin ficewa a kalla shekara guda kafin zartas da hakan, da ci gaba da biyan cikakkun kudaden karo-karo da ke wuyanta a cikin wannan wa'adi. (Saminu Hassan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China