Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta amsa kiran 'yan kasar na yin garambawul a majalisar ministoci
2020-07-10 10:05:44        cri
A ranar Alhamis majalisar mulkin kasar Sudan ta sanar da yin garambawul ga majalisar ministocin kasar domin amsa kiraye-kirayen da al'ummar kasar suka yi na neman aiwatar da sauye-sauye a tsarin shugabancin kasar.

A sanarwar da majalisar shugbancin kasar ta fitar ta ce, dukkan ministocin gwamnatin rikon kwaryar kasar su mika takardunsu na yin murabus domin baiwa gwamnatin kasar damar yin sauye-sauyen da suka dace.

Firaministan Sudan Abdalla Hamdok, ya amince da bukatar yin murabus na ministocin kasar 6, da suka hada da ministan harkokin waje, ministan kudi, ministan makamashi da hako ma'adanai, da ministan aikin gona da albarkatun kasa, da na ayyukan more rayuwa da sufuri, da kuma ministan kula da albarkatun dabbobi na kasar.

Sanarwar ta ce, Hamdok ya kuma yanke shawarar sallamar Akram Ali Al-Tom daga mukamin ministan lafiyar kasar.

Haka zalika, Hamdok ya nada shugabannin riko a guraben ministocin da lamarin ya shafa. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China