Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan za ta yi koyi daga nasarorin da Sin ta samu a yaki da COVID-19
2020-06-05 11:19:26        cri
Wani babban jami'in kasar Sudan ya sanar cewa, nasarorin da kasar Sin ta samu wajen dakile annobar COVID-19 zai kasance a matsayin babban darasi wanda kasar Sudan zata yi amfani dashi domin dakile annobar a kasar.

A sanarwar da majalisar zartarwar kasar Sudan ta fitar, Siddiq Tawer, mamba a majalisar, kana shugaban babban kwamitin ayyukan lafiya na gaggawa na kasar, yayi wannan tsokaci a lokacin ganawa da tawagar kwararrun likitocin kasar Sin da suka ziyarci kasar.

An rawaito Tawer na cewa, ziyarar da tawagar kwararrun jami'an lafiyar kasar Sin suka kai kasar ya kara nuna karfin dangantakar dake tsakanin Beijing da Khartoum.

Ya kara da cewa, nasarorin da kasar Sin ta samu wajen dakile annobar COVID-19 zai yi matukar taimakawa kasar Sudan, inda kasar zata yi amfani da nasarorin da kasar Sin ta samu a matsayin abin koyi a yakin da take yi da annobar.

Zhou Lin, shugaban tawagar kwararrun jami'an lafiyar Sin, yace kwararrun na kasar Sin sun yi musayar kwarewa da takwarorinsu na kasar Sudan a bangarorin bincike game da cutur, da aikin jiyya da kuma kandagarkin annobar kana da kuma yadda za'a dakile cutar cikin kankanin lokaci. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China