Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
UNICEF ta yi maraba da matakin gwamnatin Sudan na hukunta masu yin kaciyar mata
2020-05-03 16:12:58        cri

Asusun tallafawa kananan yara na MDD (UNICEF) ya yi maraba da matakin da gwamnatin rikon kwaryar Sudan ta dauka mai cike da tarihi a makon jiya na amincewa da hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari ga masu yin kaciyar mata.

Abdullah Fadil, wakilin hukumar UNICEF a Sudan ya ce, wannan al'ada ba kawai tana take hakkin yara mata ba ne, har ma tana haifar da mummunar illa ga lafiyar kananan yara mata kana tana taba lafiyar tunaninsu.

Ya kara da cewa, tilas ne gwamnati da al'umma su gaggauta daukar mataki domin kawo karshen wannan al'ada. Wannan mataki ya zo ne bayan shafe shekaru masu yawa kungiyoyi masu fafutukar suna ta yin kiraye kirayen yaki da al'adar, daga ciki akwai majalisar kare lafiyar kananan yara ta Sudan, da kungiyar kare hakkin mata da kananan yara, da kungiyoyin MDD da na kasa da kasa da kungiyoyin fafutuka dake kasar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce, kididdiga ta nuna cewa, sama da yara mata miliyan 200 a fadin duniya ake yiwa kaciyar mata a kasashen duniya da ake yin wannan al'ada. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China