Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan za ta bude filin jiragen saman Khartoum ga Masar, Turkiyya da UAE
2020-07-10 10:04:50        cri
Hukumar kula da filayen jiragen saman kasar Sudan a ranar Alhamis ta yanke shawarar sake bude filin jirgin saman Khartoum ga fasinjoji daga kasashen Masar, Turkiyya da hadaddiyar daular Larabawa UAE.

A sanarwar da daraktan hukumar kula da sararin samaniyar kasar Ibrahim Adlan ya fitar an ce, an dauki wannan mataki ne bayan shawarar da babban kwamitin ayyukan kiwon lafiyar gaggawa na kasar ya zartar game da farfado da harkokin yau da kullum sannu a hankali.

Ya kara da cewa, kasashen Masar, Turkiyya da UAE, sun riga sun sanar da bude filayen jiragen saman su domin baiwa Sudan damar hulda da su ta hanyar jiragen saman kasar ko kuma kamfanonin jiragen saman wadannan kasashe uku.

Adlan ya kara da cewa, dukkan fasinjojin da suka isa filin jirgin saman Khartoum za su bi ka'idojin hukumar lafiya, yayin da su ma 'yan kasar Sudan ko 'yan ciranin da aka maido da su kasar za'a yi musu gwaje-gwajen lafiya a filin jirgin saman. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China