Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sudan ta yaba da tallafin kasar Sin na yaki da COVID-19
2020-06-10 12:00:36        cri

Gwamnatin Sudan ta bayyana godiya da tallafin kasar Sin, ga kokarin da take na dakile annobar COVID-19.

Mamban majalisar gwamnatin riko na Sudan, kuma shugaban kwamitin kiwon lafiya na gaggawa, Siddiq Tawer ne ya bayyana haka, lokacin da ya karbi tawagar jami'an lafiya ta kasar Sin dake ziyara a kasar, a fadar shugaban kasa dake birnin Khartoum.

Cikin wata sanarwa, Siddiq Tawer, ya ce sun yi farin ciki da ziyarar tawagar, wadda ya ce sun amfana da ita matuka.

Tawagar ta kuma je kasar da kayayyakin lafiya na yaki da COVID-19, ciki har da kayayyakin dakin gwaji da rigunan kariya da sauran kayayyakin yaki da annobar.

Shugaban tawagar Sinawan, Zhou Lin, ya ce ziyarar tawagar ta nuna karfin dangantakar abota dake tsakanin Sin da Sudan.

Ya ce cikin makonni biyu da suka gabata, sun fahimci damuwar gwamnati da ma'aikatar lafiya ta kasar, ta aiwatar da matakan kandagarki domin yaki da COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China