Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan kasar Sin ya karyata zancen da wasu kasashe suka yi game da yankunan Xinjiang da Hongkong
2020-02-29 16:37:31        cri
Jiang Duan, ministan kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva, da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Switzerland, ya yi jawabi a taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD, inda ya karyata zancen da wasu kasashe suka yi dangane da yankunan Xinjiang da Hongkong na kasar Sin.

Jiang Duan ya ce, batun Xinjiang bai shafi hakkin dan Adam, ko addini, ko kabilanci ba, yana mai cewa, hakika batu ne da ya shafi kokarin kasar Sin a fannin dakile ta'addanci da 'yan a-ware. Ya ce yanzu haka, jihar Xinjiang na daukar matakan kawar da ra'ayin ta'addanci da na kaifin kishin addini, ciki har da kafa wasu cibiyoyin koyar da ilimin sana'o'i, inda take samun nasara sosai. Jiang Duan ya ce kasar Sin na fatan ganin babbar kwamishina mai kula da batun hakkin dan Adam, VerĂ³nica Bachelet ta ziyarci kasar Sin a bana, gami da rangadi a jihar Xinjiang. Ban da haka, ya ce kasar Sin ta gayyaci jakadun wasu kasashen nahiyar Turai dake kasar, don su ziyarci jihar Xinjiang sau da dama, amma wadannan jakadun su kan fake da wasu dalilai don su ki zuwa. Ministan ya kara da cewa, kasashen ba sa son ziyartar Xinjiang, amma duk da haka suna ta zargin kasar Sin da keta hakkin bil Adama a jihar, hakan ya sa ake tuhumar ainihin abin da suke nema.

Dangane da maganar Hongkong, Jiang Duan ya ce, daya ce daga cikin harkokin gidan kasar Sin, don haka kasar ba za ta yarda wata kasa ta tsoma mata baki ba. Tun daga watan Yunin bara, ake ta samun aikace-aikacen nuna karfin tuwo, wadanda suka kasance laifukan da suka keta dokoki da tsarin al'umma, da gurgunta tattalin arzikin yankin Hong Kong, gami da haifar da barazana ga babbar manufar kasar Sin ta "Kasa daya mai tsarin mulki 2". A cewar Jiang, wasu kasashe sun yi biris da hare-haren da 'yan bore suka yi ta kai wa 'yan sanda, da yadda suke tsoratar da 'yan sandan da iyalansu, amma suna ta yada jita-jita game da 'yan sandan Hongkong, duk da cewa sun yi hakuri sosai. Hakan ya nuna cewa, wadannan kasashe na nuna bambanci kan lamarin.

Saboda haka Jiang Duan ya bukaci wasu kasashe da kungiyoyi, su daina nuna bambanci, da girman kai, gami da yin watsi da yunkurinsu na shafa wa kasar Sin bakin fenti. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China