Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harkokin nishadantarwa na unguwanni suna bunkasa jin dadin zaman rayuwar alumma
2020-07-09 12:38:09        cri

Da safiyar ko wace rana, Wu Lili da abokan raye-rayenta, su kan yi rawa a wani filin dake cikin unguwarsu, a titin Jiefang na birnin Zhumadian dake lardin Henan na kasar Sin.

Wannan yanki na cike da tsoffin unguwanni da gine-gine, amma, ofishin kula da harkokin unguwanni, ya samar wa kungiyar raye-rayen dake karkashin jagorancin Wu Lili wani fili mai fadi, don su rika yin rawa.

A shekarar 2016, ofishin kula da harkokin unguwannin dake titin Xiyuan na yankin Yicheng, ya tattara kudade domin gyara titunan yankin, sa'an nan, ya gayyaci kungiyar 'yan wasan fasaha da ta ba da taimako wajen kyautata zaman rayuwar al'ummomin yankin.

Cikin ko wane mako, Wu Lili ta kan saurari jawabai a unguwar, wadanda suka shafi harkoki daban daban, kamar harkokin kasa da kasa, da manufufin tallafawa al'umma, har ma da shirye-shiryen raya unguwar, ko kuma gabatarwa kan wani littafi mai ban sha'awa da dai sauransu.

Da take tsokaci kan unguwar da take da zama, Wu Lili ta ce, ta gamsu sosai, sabo da ba ta damuwa ko kadan ta fuskar bukatun yau da kullum, kamar samun abinci da tufafi, tana kuma da inshorar jinya da sauransu. Unguwarta ta kuma gayyaci masana don su koyar musu fasahohin rera wakoki ba tare da karbar kudade ba.

A ganinta, cikin 'yan shekarun nan, ofishin unguwanni ya kara ba da taimako ga mazauna yankin, musamman ma a wannan lokacin da ake fama da annobar cutar numfashi ta COVID-19.

Bugu da kari, a cikin unguwarta, har ma da duk fadin yankin da take da zama, ba wanda ya kamu da cutar. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China