Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin: Akwai hanyoyi da dama wajen cimma burin kare hakkin bil Adama
2020-02-27 12:08:47        cri

Jiya Laraba, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD dake birnin Geneva, kana wakilin kungiyoyin kasa da kasa dake kasar Switzerland, Chen Xu ya bayyanawa taron manyan jami'an kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD karo na 43 da aka gudanar cewa, bana, shekaru 75 da kafuwar MDD, kuma babban burin kasashen duniya, shi ne tabbatar da zaman lafiya da neman ci gaba, amma, yanzu ana fama da tashe-tashen hankula a wasu kasashen duniya, ana kuma kara nuna ra'ayin kariyar ciniki, lamarin da ya haifar da kalubaloli ga harkokin kasa da kasa dake karkashin jagoranci na MDD.

Chen Xu ya ce, akwai hanyoyi daban daban da za mu iya bi wajen cimma burinmu na kare hakkin bil Adama, ya kamata mu martaba 'yancin kasashe na zabar hanyar da suke so bisa halin da suke ciki da kuma bukatun al'ummar kasashensu, ba sai mun tsara hanyar da za mu tilastawa kasa bi ba, wannan ba adalci ba ne. Bugu da kari, ba za mu iya samun dauwamammen ci gaba kan harkokin kare hakkin dan Adam ba, sai mun martaba ka'idojin kundin tsarin MDD, da girmama tsarin kasashe game da da hanyar da suke bi wajen kiyaye hakkin dan Adam, da raya mu'amala da hadin gwiwar kasa da kasa, da kuma daina mayar batun kare hakkin da Adam a matsayin batun siyasa, da ma daina nuna bambanci da yin fuska biyu kan batun kare hakkin dan-Adam. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China