Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jami'in Sin: Kasar Sin tana martaba 'yancin dan-Adam
2019-12-11 20:47:28        cri

Mamba a hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, kana shugaban sashen fadakar da jama'a na kwamitin koli na JKS Huang Kunming, ya bayyana cewa, JKS da gwamnatin kasar suna martaba tare da kare 'yancin dan-Adam., saboda muhimmancinsu ga wayewar kan bil-Adam.

Huang Kunming ya bayyana haka ne, yayin da yake da jawabi a taron dandalin kasashe masu tasowa game da kare 'yancin bil-Adama.

Ya ce, har kullum JKS tana daukar batun da ya shafi jin dadin jama'a da muhimmancin gaske, kana manufar tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin a kullum shi ne, kare muradun jama'a. Huang ya ce, kasar Sin tana bin hanyar bunkasuwa da ta dace da hakikanin halin da ake ciki, ta kuma koyi abubuwa da dama a cikin shekaru 70 din da suka gabata. A don haka, ya yi kira ga kasashe masu tasowa, da su hada kai don samun ci gaba a kokarin da ake na kare hakkin bil-Adama tare da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China