Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen dake tasowa sun jaddada muhimmancin neman ci gaba ga kare hakkin dan Adam
2019-09-13 16:19:27        cri
An yi shawarwari da masu gabatar da rahoto na musamman kan ikon neman bunkasuwa, a yayin taro karo na 42 na hukumar kula da hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ko UNHRC a takaice.

Wakilin kasar Sin ya bayyana cewa, wani muhimmin fanni na aikin kare hakkokin dan Adam na kasar Sin shi ne, tsayawa ga rayawa, gami da kare hakkin dan Adam, yayin da kasar ke neman bunkasuwa.

Ya ce kasar Sin ta samar da isasshen abinci ga mutanenta da yawansu ya zarce biliyan 1.4, ta kuma rage adadin mutanen da suke fama da talauci da yawansu ya kai miliyan 850, tare kuma da samar da guraban ayyukan yi ga mutane kimanin miliyan 770.

Har wa yau, kasar Sin ta yi nasarar kafa tsarin samar da ilimi mafi girma, da tsarin samar da inshorar ganin likita, da bada tabbacin zaman rayuwa ga al'umma mafi girma a duk duniya.

Ya ce a nan gaba kuma, Sin za ta ci gaba da bada gudummawa ga ci gaban tattalin arzikin duniya, da samar da damammakin bunkasa ga al'ummar duniya baki daya.

A nasu bangaren, wasu kasashen dake tasowa, ciki har da Angola, da Afirka ta Kudu, da Masar, da Pakistan sun jaddada cewa, ikon neman bunkasuwa wani muhimmin fannin ne na hakkin dan Adam, amma tun da dadewa, kasashen duniya gami da hukumomin kare hakkin dan Adam na MDD, ba su maida hankali sosai kan batun neman bunkasuwa ba, wanda hakan ya sa har yanzu, ba'a aiwatar da sanarwa kan ikon neman bunkasuwa ta MDD yadda ya kamata ba, duk da cewa an amince da ita shekaru sama da 30 da suka gabata.

Wadannan kasashe sun bukaci hukumar UNHRC ta kara bada fifiko kan ikon neman bunkasuwa, da gaggauta nazari, gami da tsara takardun doka a wannan fanni, a wani kokari na rage gibin bunkasuwa tsakanin kasashe daban-daban.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China