Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da dandalin nahiyar Afrika na kungiyar wasan kwallon tebur ta kasa da kasa
2020-07-09 10:38:10        cri
An gudanar da dandalin nahiyar Afrika na kungiyar wasan kwallon tebur ta kasa da kasa wato WTT ta Intanet a jiya Laraba. Shugaban kungiyar wasan kwallon tebur Liu Guoliang, a karo na farko, ya halarci dandalin a matsayin shugaban kwamitin gudanarwar WTT, inda kuma ya gabatar da jawabi. Shugabannin kungiyoyin wasan kwallon tebur na kasashen Afrika da sauran muhimman jami'ai sun halarci dandalin.

A cikin jawabinsa, Liu Guoliang ya ce, 'yan wasan kwallon tebur, da kuma masu kaunar wasan, su ne tushen kungiyar WTT, kuma kungiyar za ta ci gaba da kara tuntubar Afrika.

A cikin jawabinsa, babban jami'in gudanarwa na WTII Steve Danton, ya bayyanawa mahalarta taron daga nahiyar Afrika na kungiyar ta WTT, irin bunkasuwar wannan wasa a nahiyar Afrika. Ya ce, WTT na shirin tura 'yan wasan Afrika wuraren samun horo tare da 'yan wasan kasar Sin mafiya kwarewa, kuma suna shirin kara bunkasa wannan wasa a nahiyar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China