Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin kasar Sin ta yarda WHO ta turo kwararrunta zuwa kasar
2020-07-08 21:06:51        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Laraba cewa, bayan da suka yi shawarwari, gwamnatin Sin ta yarda WHO ta tura kwararrunta zuwa Beijing, domin yin musanyar ra'ayi tare da takwarorinsu na kasar Sin kan batutuwan da suka shafi binciken asalin kwayar cutar COVID-19 cikin hadin-gwiwa.

A game da wannan batu, Mista Zhao Lijian ya bayyana cewa, binciken asalin kwayar cutar batu ne da ya shafi kimiyya, wanda ke bukatar masana kimiyya da kwararrun likitoci su yi nazari cikin tsanaki. A cikin jawabin da ya gabatar a wajen bikin bude babban taron lafiya na duniya karo na 73, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, kasarsa za ta ci gaba da nuna goyon-baya ga masana da kwararru na kasa da kasa don su gudanar da bincike cikin hadin-gwiwa kan ainihin yadda kwayar cutar ta samo asali gami da hanyoyin bazuwarta.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China