Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin:Matakin Amurka na dakatar da ba da kudaden da take baiwa WHO zai lalata alakar kasa da kasa kan yaki da COVID-19
2020-04-15 20:32:23        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana cewa, shawarar da Amurka ta yanke na dakatar da ba da kudaden da take baiwa hukumar lafiya ta duniya(WHO), za ta kawo illa ga hadin gwiwar kasashen duniya na yaki da cutar COVID-19, kuma kasar Sin ta damu matuka kan wannan batu.

Ya ce, kasancewar ta kwararriyar hukumar kasa da kasa kuma mai fada aji a fannin kiwon lafiyar al'ummar duniya, WHO ta taka muhimmiyar rawa wajen yaki da matsalar kiwon lafiyar al'ummar duniya.

Zhao ya bayyana haka ne lokacin da aka tambaye shi, yayin taron manema labarai, kan shawarar da shugaba Donald Trump ya sanar a ranar Talata. Yana mai cewa, idan aka yi la'akari da muni da yanayin annobar a duniya, shawarar da Amurka ta yanke na dakatar da bayar da kason kudaden, zai raunata hukumar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China