Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta amsa kiran WHO game da aiwatar da hadin gwiwar kasa da kasa
2020-05-06 20:24:15        cri
Mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, Madam Hua Chunying, ta bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin za ta karbi shawarar da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayar, dangane da aiwatar da hadin gwiwar kasa da kasa, za kuma ta hada gwiwa da kasa da kasa, don gaggauta nazarin kayayyakin jinyar masu cutar Covid-19, don ba da gudummawarta wajen kare lafiyar al'ummar duniya.

Jami'ar ta kara da cewa, bayan barkewar cutar, kasar Sin ta raba bayanai kan nazarin kwayoyin halittar cutar da kasashen duniya cikin lokaci, kuma tana kokarin hada gwiwa da kasa da kasa, wajen nazarin magunguna da alluran rigakafin cutar, ta kuma ba da babbar gudummawarta a wannan fanni.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China