Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Janyewar Amurka daga WHO zai illata kokarin kasa da kasa na dakile COVID-19
2020-07-08 21:02:03        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau Laraba cewa, matakin Amurka na janyewa daga hukumar lafiya ta duniya wato WHO, zai illata kokarin kasa da kasa na yaki da cutar COVID-19, musamman zai haifar da mummunar illa ga kasashe masu tasowa, wadanda ke bukatar taimako na gaggawa.

Rahotannin da aka ruwaito na cewa, a jiya ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana cewa, shugaba Donald Trump ya sanar da babban sakataren MDD Antonio Guterres cewa, ya riga ya fara shirin janye kasarsa daga WHO, kakakin Guterres ya tabbatar da maganar.

Mista Zhao Lijian ya ce, kasar Sin ta bukaci Amurka ta sauke nauyin dake wuyanta yadda ya kamata, musamman a matsayinta na babbar kasa. Sin ta kuma yi kira ga kasashen duniya, da su kara cimma ra'ayi daya, wato kasancewar bangarori daban-daban a duniya, da ci gaba da zuba kudi da nuna goyon-baya ga WHO, a wani mataki na kiyaye lafiyar al'ummomin duniya.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China