Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yunkurin Taiwan na fakewa da sunan annoba domin shirya manakisar siyasa ba zai yi nasara ba
2020-05-09 21:57:49        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a jiya cewa, yunkurin Taiwan na zama mamban hukumar lafiya ta duniya WHO, fakewa ne da sunan yaki da annobar COVID-19, wajen shirya manakisar siyasa, kuma ba zai yi nasara ba.

Ta ce abun da kowa ya sani ne cewa, a watan Oktoban 1971, zauren MDD na 26, ya amince da kuduri mai lamba 2758, dake bayyana gwamnati Jamhuriyar Jama'ar Kasar Sin, a matsayin halaltacciyar gwamnatin dake wakiltar kasar Sin.

Ta ce manufar kasar Sin daya tak a duniya kuma Taiwan wani yanki nata ne da ba zai iya ballewa ba, abu ne da kasashen duniya suka amince da shi. Kuma MDD ta sha nanata cewa, tana son a rika tafiyar da batutuwan da suka shafi Taiwan bisa kudurin mai lamba 2758, inda Hua ta kara da cewa, a matsayinta na hukumar dake karkashin MDD, ya kamata WHO ta kiyaye kudurin babban zauren majalisar. (Fa'izaMustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China