Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin a shirye take ta samarwa WHO ingantattun ayyukan hidima
2020-05-07 20:33:38        cri
Mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce har kullum, Sin a shirye ta ke, da ta samarwa hukumar lafiya ta duniya WHO, managarta, kuma kyawawan hidimomi, za ta kuma ba da tata gudummawa ga ayyukan da kasashen duniya ke yi, na yaki da annoba cikin hadin gwiwa.

Hua Chunying, wadda ta bayyana hakan yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa a nan birnin Beijing a yau Alhamsi, ta ce kamfanonin kasar Sin da dama na shiga ayyukan hadin gwiwa tare da WHO. Kaza lika gungun kamfanonin harhada magunguna na kasar Sin, sun yi matukar tallafawa hukumar, wajen samar da isassun kayan kandagarkin cutar COVID-19 a cikin kasar ta Sin.

Ta ce a baya bayan nan, sassan biyu, sun sanya hannu kan wata yarjejeniya, ta tantance adadin kayayyakin da ake samarwa, da cinikayyar su, da fannin adana kayan, da dai sauran hidimomi masu nasaba da sayayyar da WHOn ke yi a kasar Sin. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China