Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO da kwararrun kasar Sin sun fara aikin bincike kan cutar numfashi ta COVID-19
2020-02-18 11:17:56        cri

Tawagar hadin gwiwa wadda ta kunshi kwararrun kasar Sin da na hukumar lafiya ta duniya WHO a ranar Litinin sun fara aikin rangadin bincike game da ayyukan kandagarki da dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19, jami'in hukumar lafiyar kasar Sin ya tabbatar da hakan.

Mi Feng, kakakin hukumar lafiyar kasar Sin (NHC), ya fada a taron manema labarai cewa, tawagar kwararrun za su fara ne da ziyartar Beijing, da lardunan Guangdong da Sichuan domin duba yadda ayyukan yaki da cutar ke gudana.

A ranar Lahadi NHC ta shirya taron karawa juna sani, wanda ya samu halartar kusan mutane 80, da ya kushi tawagar hadin gwiwa ta kwararru da wakilan mambobin majalisar gudanarwar kasar Sin dake tafiyar da ayyukan kandagarki da kawar da annobar, in ji Mi.

A lokacin gudanar da taron karawa juna sanin, mataimakin daraktan hukumar NHC Li Bin, ya yi wa mahalarta taron takaitaccen jawabi game da matakan ayyukan kandagarki da yaki da annobar wanda ake gudanarwa a duk fadin kasar, ya jaddada cewa a shirye suke su yi aiki da bangarorin kasa da kasa domin tinkarar kalubalolin yaki da annobar, kuma suna maraba da duk wasu shawarwarin da tawagar kwararrun zasu gabatar.

Mi ya kara da cewa tawagar kwararrun ta hadin gwiwa sun nuna gamsuwa da irin matakan da kasar Sin ke dauka wajen kandagarki da kawar da cutar, da kuma yadda Sinawa ma'aikatan lafiya suka sadaukar da kansu don tinkarar ayyukan yaki da annobar cutar numfashin ta COVID-19. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China