Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Najeriya ya yi ban kwana da shugaba Buhari
2020-07-08 10:35:59        cri

Jiya Talata, jakadan kasar Sin dake Najeriya Zhou Pingjian ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari ta kafar Intanet, don yin ban kwana da shi.

Yayin ganawar tasu, Zhou Pingjian ya ce, a shekarun baya bayan nan, kasashen biyu sun kara amincewa da juna a siyasance, tare kuma da samun ci gaba mai armashi wajen hadin kansu, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, da ma nagartattun tsare-tare.

Ya ce, dangantakar kasashen biyu na cikin wani lokaci mafi kyau a tarihi. Sin kuma tana darajanta matsayin da Najeriya take dauka na nacewa ga tsarin "kasa daya mai tsarin mulki iri biyu", da kuma mutumta ikon mulkin kasar Sin kan harkokin dake da alaka da yankin Taiwan, da Hon Kong da dai sauransu.

Kaza lika Sin na dora babban muhimmanci kan dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, tana kuma fatan kara hadin kai da Najeriya, wajen ingiza tabbatar da ci gaban da aka samu, a yayin taron koli na Beijing na dandalin tattauna hadin kan Sin da Afrika, da ma taron musamman na hadin kan Sin da Afrika game da yakar COVID-19, ta yadda za a kara bunkasa dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare zuwa wani sabon matsayi, don amfanin jama'ar kasashen biyu.

A nasa bangare, shugaba Buhari ya nuna cewa, Najeriya da Sin na da dankon zumunci na kut da kut. Ya ce an tabbatar da matsaya daya da shugabannin biyu suka cimma a yayin ziyararsa a kasar Sin, musamman ma a fannin hadin kai ta fuskar samar da manyan ababen more rayuwa.

Shugaba Buhari ya ce Sin ta ba da babbar gudunmawa, wajen biyan bukatun Najeriya ta fuskar inganta layin dogo na jiragen kasa, da hanyoyin motoci, da kuma filayen saukar jiragen sama, da wutar lantarki da dai sauransu, wadanda Najeriya ke karancin su. Saboda haka, yana godiya sosai ga shugaba Xi Jinping, da gwamnatinsa, da ma jama'ar kasar Sin.

Har ila yau, Najeriya tana fatan kara hadin kai da kasar Sin, wajen kara ingiza bunkasuwar dangantakar kasashen biyu zuwa matsayi na gaba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China