Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban hafsin sojojin Najeriya ya jaddada aniyar yaki da 'yan bindiga a yankin arewa maso yammacin kasa
2020-07-01 19:59:53        cri
Babban hafsin sojojin Najeriya Tukur Buratai ya jaddada aniyar sojon kasar, na ci gaba da yaki da 'yan bindiga, a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Buratai wanda ya sha wannan alwashi, yayin da yake jawabi ga dakarun rundunar sojojin dake aiki a birnin Gusau, fadar mulkin jihar Zamfara a jiya Talata, ya ce yanayi mai sarkakiya na yakin da rundunarsa ke yi da 'yan bindiga a wannan yanki, na bukatar kara zage damtse wajen kawar da 'yan ta'addar.

Daga nan sai ya kara yin kira ga sojojin, da su fadada ayyukansu, domin kaiwa ga dukkanin sassan dazukan dake wannan yanki, musamman wuraren da bata-gari masu dauke da makamai ba bisa ka'ida ba ke samun mafaka, domin murkushe su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China