![]() |
|
2020-07-04 15:51:46 cri |
Rundunar sojin Nijeriya, ta ce an kashe mayakan BH da dama yayin wani luguden wuta a dajin Sambisa dake jihar Borno, a yankin arewa maso gabashin kasar.
Kakakin rundunar John Enenche da ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, ya ce sojoji sun kuma lalata inda kungiyar ke taruwa a Mainyakare dake yankin dajin Sambisa.
Dajin Sambisa ya yi kaurin suna a matsayin sansanin horo mafi girma na kungiyar BH a Nijeriya.
John Enenche ya kara da cewa, harin sojojin ya gudana ne a ranar Alhmis, biyo bayan jerin bayanan sirri, wanda kuma wani bangare na hare-hare ta sama da rundunar ke ci gaba da kaiwa, da nufin karya lagon kungiyar. (Fa'izaMustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China