Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sanya ranar sake bude filayen jiragen saman Najeriya
2020-07-02 10:55:13        cri
Ministan kula da harkokin zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya Hadi Sirika, ya bayyana cewa, nan ba da dadewa ba za a sake bude filayen jiragen saman kasar da aka rufe sakamakon annobar COVID-19.

Ministan wanda ya bayyana haka cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tiwita, ya ce jirage za su fara tashi da sauka a filayen jiragen saman Abuja da Lagos a ranar 8 ga watan Yuli, yayin da za a bude sauran filayen jiragen saman kasar tsakanin ranakun 11 da 15 ga watan na Yuli.

Sau biyu ne dai mahukuntan Najeriyar ke duba yiwuwar sake bude filayen jiragen saman kasar, amma hakan bai yiwu ba. A ranar 23 watan Maris ne dai, gwamnatin Najeriyar ta rufe filayen jiragen saman, a wani mataki na yaki da annobar COVID-19. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China