Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnan jihar Delta a Najeriya ya kamu da COVID-19
2020-07-02 09:18:33        cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, gwamnan jihar Delta dake yankin kudancin kasar Ifeanyi Okowa ya kamu da cutar COVID-19.

Da yake karin haske cikin wata sanarwa, mai magana da yawun gwamnan Olisa Ifeajika, ya bayyana a jiya Laraba cewa, sakamakon binciken da aka yiwa gwamnan da mai dakinsa Edith ne ya tabbatar da haka. An fara yiwa gwamnan da mai dakinsa jinyar cutar, kuma ba sa cikin matsanancin yanayi.

Tun da farko dai gwamnan da mai dakinsa sun kebe kansu, bayan da sakamakon gwajin da aka yiwa 'yarsu a makon da ya gabata ya tabbatar da cewa, ta kamu da cutar.

Ifeajika, ya ce gwamnan ya ba da tabbatacin cewa, gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba, a kokarin da take yi na yakar cutar a jihar. A don haka, ya bukaci al'ummar jihar, da su baiwa gwamnatinsa goyon baya a wannan fanni, ta hanyar bin shawarwarin hukumar dakile cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC). (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China