Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dakarun sojin Najeriya sun hallaka wasu 'yan bindiga a jihar Sokoto
2020-07-08 10:34:25        cri
Rundunar sojojin saman Najeriya, ta ce dakarunta sun yi luguden wuta kan wasu sansanonin 'yan bindiga dake addabar al'umma, wadanda ke samun mafaka a dajin Kagara na jihar Sokoto, a arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya sabbasa kisan 'yan bindiga da dama, tare da lalata sansanonin su.

Cikin wata sanarwar da ya fitar, shugaban rundunar sojin saman kasar Sadique Abubakar, ya shaiwada manema labarai hakan jiya Talata, yana mai cewa, hare-haren na ranar Litinin, daya ne daga matakan da ake dauka, na kakkabe yankin daga ayyukan 'yan bindiga, da 'yan fashin shanu, da masu garkuwa da mutane, da ma sauran masu aikata laifuka dake addabar al'ummar yankin.

Sadique Abubakar, ya kara da cewa, da yake dajin Kagara ya dangana zuwa janhuriyar Nijar, dakarun Najeriyar na aiki kafada da kafada da takwarorin su na Nijar, don tabbatar da 'yan bindiga ba su tsere ta kan iyakokin kasa da kasa yayin da ake fatattakar su ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China