Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasashen Afirka wajen yakar Covid-19
2020-05-24 19:19:26        cri

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, wanda kuma shi ne ministan harkokin waje na kasar, Mr. Wang Yi, ya bayyana a yau Lahadi cewa, kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa Afirka a yaki da cutar Covid-19, tare da rage basusukan da ake binsu.

A gun taron manema labarai da aka shirya a wannan rana a fagen taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin da ke gudana a nan birnin Beijing, Mr. Wang Yi ya ce, a yayin da ake tsaka da yaki da cutar Covid-19, Sin da kasashen Afirka za su ci gaba da hada kan juna, kuma kasar Sin zata ci gaba da samar da gudummawarta ga kasashen Afirka, za ta kuma baiwa kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa fifiko wajen samar musu gudummawar kayayyakin jinya, tana kuma shirin tura sabon ayarin jami'an lafiya zuwa Afirka.

Ban da wannan, Wang Yi ya kuma jaddada cewa, kasar Sin zata yi kokarin aiwatar da shawarar kungiyar G20 ta "saukaka basusukan da ake bin kasashen Afirka", don saukaka wahalar da suke fuskanta ta fannin basusuka. Tana kuma shirin kara samar da gudummawa ga kasashen Afirka da suke matukar fuskantar matsala, don taimaka musu haye wahalhalun.(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China