Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan harkokin wajen Sin yayi jawabi game da abu mafi muhimmanci a yaki da COVID-19 a duniya
2020-05-24 17:12:48        cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya ce abu mafi muhimmanci da ya kamata a koya daga annobar COVID-19 shi ne, jama'ar kasashen duniya daban dabanna matukar alaka da juna ta fannonin rayuwarsu da lafiyarsu.

Haka zalika, an sake lura a bayyane cewa dukkan kasashen duniya suna rayuwa ne a matsayin al'ummar gari guda kuma wannan al'umma tana da makoma iri guda, Wang ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a gefen taron majalisar wakilan jama'ar kasar na wannan shekara.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China