Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a shirya taron hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar Ziri daya da hanya daya
2020-06-16 19:42:34        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijiang ya sanar a yau Talata cewa, za a shirya taron manyan jami'an hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar Ziri daya da hanya daya ta kafar bidiyo.

Taken taron, wanda za a gudanar a jibi Alhamis 18 ga watan Yunin da muke ciki, shi ne " Karfafa hadin gwiwar kasa da kasa kan Shawarar Ziri daya da hanya daya gami da hada kai don yaki da COVID-19".

Mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, shi ne zai jagoranci taron. A hannu guda kuma, ministocin harkokin waje ko jami'an ma'aikatar daga kasashe 25 gami da manyan jami'ai daga MDD da hukumar lafiya ta duniya WHO ne, ake sa ran za su halarci taron.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China