Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nazari kan yadda aka kafa "kungiya mafi samun ci gaba a tarihi" a kasar Sin
2020-07-01 21:51:26        cri

A watan Fabrairu na shekarar 2019, hukumar NASA ta kasar Amurka ta sanar da cewa, taurarin dan Adam nata sun gano cewa, launin kore yana kara bazuwa a duniyarmu, bisa babbar gudummawar da kasar Sin da kasar Indiya suka bayar.

 

 

Fadin yankin daji yana karuwa a kasar Sin, wanda ya karu daga kaso 9% kan na shekarar 1949 zuwa 23% a yanzu, an kuma cimma nasarar dakile zaman hamada a kasar, mutane sama da miliyan 70 dake zama a yankunan rashin albarkatun kasa sun cimma nasarar kawar da talauci.

Kasar Sin ta cimma sakamako da dama a fannin kiyaye muhalli, a sa'i daya kuma, ta halarci aikin kyautata muhalli na kasa da kasa cikin himma da kwazo, domin ba da gudummawa ga samun dauwamammen ci gaban kasashen duniya. Cikin shekaru sama da 40 da suka gabata, masanin daidaita gurbataccen tabki na kasar Japan Yuhei Inamori, ya kan kawo ziyara kasar Sin cikin ko wace shekara. Yana ganin cewa, kasar Sin tana karfafa ayyukan kiyaye muhalli, lamarin da ya sa, muhallin kasar Sin ke ci gaba da samun kyautatuwa, ta yadda za a samu daidaituwa a tsakanin mutane da muhallin halittu.

1  2  3  4  5  6  7  8  9  10  11  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China