Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nazari kan yadda aka kafa "kungiya mafi samun ci gaba a tarihi" a kasar Sin
2020-07-01 21:51:26        cri

Yawan kasashen da suka shiga shirin hadin gwiwa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya" yana ta karuwa. Ya zuwa shekarar 2019, yawan takardun hadin gwiwa masu nasaba da hakan sun kai 200. Lamarin da ya bayar da gudummawa ga duniya a fannonin tinkarar kalubale, da samar da dama, da ma karfafa zuciya. Ya zuwa watan Maris na shekarar 2019, Sin da kasashen da suka sa hannu cikin shirin, sun gina cibiyoyin hadin kai guda 82 a ketare, inda Sin ta biya kudin haraji fiye da dala biliyan 2, yayin da take samar da guraban ayyukan yi kimanin dubu 300 ga mazauna wadannan wuraren.

David Monyae, shugaban cibiyar nazarin dangantakar da ke tsakanin Afirka da Sin da ke kasar Afirka ta Kudu ya nuna cewa, shawarar "ziri daya da hanya daya", ta kasar Sin ce, kuma ta duniya ce baki daya. Wadda ta dace da Ajandar AU ta shekarar 2063, da hada burin ci gaban Sin da Afirka gu daya. Shawarar kuma za ta iya biyan bukatun bunkasuwar nahiyar Afirka.

1  2  3  4  5  6  7  8  9  10  11  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China