Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nazari kan yadda aka kafa "kungiya mafi samun ci gaba a tarihi" a kasar Sin
2020-07-01 21:51:26        cri

 

A cikin shekaru fiye da 40 da suka gabata, tun daga karshen shekaru 70 na karnin da ya gabata, jam'iyyar kwaminis ta Sin, ta jagori jama'ar kasar Sin wajen yaki da talauci, da cimma nasarar kawar da talauci ga mutane fiye da miliyan 700. Yawan mutanen da suke fama da talauci a kauyukan kasar Sin ya ragu, daga kashi 97.5 cikin dari a shekarar 1978 zuwa kashi 0.6 cikin dari a shekarar 2019.

Ya zuwa karshen shekarar 2020, za a cimma burin warware matsalolin rashin abinci, da rashin tufafi da mutane masu fama da talauci a kauyuka suke fuskanta, sannan za a tabbatar da ba su ilmi, da jinya, da gidajen kwana masu inganci, don cimma nasarar kawar da kangin talauci a yankunan kauyuka.

Shugaban jam'iyyar kwaminis ta kasar Masar Salah Adly ya bayyana cewa, nasarorin kawar da talauci da Sin ta samu sun shaida cewa, jam'iyyar kwaminis ta Sin, ta tsaya kan matsayin samar da hidima ga jama'a. Jam'iyyar ta taimakawa jama'a wajen cimma burinsu, wannan shi ne dalilin da ya sa jama'a ke nuna goyon baya gare ta.

1  2  3  4  5  6  7  8  9  10  11  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China