Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nazari kan yadda aka kafa "kungiya mafi samun ci gaba a tarihi" a kasar Sin
2020-07-01 21:51:26        cri

Bayan da Xi Jinping ya zama babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin a shekarar 2012, ya yi ta kokarin tsaurara matakan ladabtarwa a cikin jam'iyyar, da dakile cin hanci da rashawa, lamarin da ya burge mutanen duniya sosai. A shekarun baya, an fi samun manyan jami'an da aka sallame su, da gurfanar da su gaban kotu a kasar Sin, sakamakon yadda aka kama su da laifin cin hanci da rashawa.

Har ma jaridar New York Times ta kasar Amurka ta taba wallafa wani sharhi mai taken "Yadda shugaban kasar Sin ke kokarin yakar cin hanci da rashawa, ya faranta wa jama'ar kasar ransu", inda aka ce yukurin dakile cin hanci da rashawa da shugaba Xi Jinping ke jagoranta, ya samar da sauki ga jama'ar kasar Sin, yayin da suke tafiyar da harkoki na yau da kullum.

Lambar 99 tana da ma'ana sosai a cikin al'adun kasar Sin, wadda ke alamantar wani sabon zagaye na wani abu. Don haka, yayin da ake murnar ranar haihuwa ta 99 ta jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, muna fatan ganin jam'iyyar za ta kasance cikin wani yanayi mai armashi, gami da dinga samun ci gaba a harkoki daban daban. (Masu Fassarawa: Kande, Zainab, Maryma, Bello)


1  2  3  4  5  6  7  8  9  10  11  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China