Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nazari kan yadda aka kafa "kungiya mafi samun ci gaba a tarihi" a kasar Sin
2020-07-01 21:51:26        cri

Xi Jinping: Ya kamata a yi duk wani kokari, wajen maida jama'a gami da rayukansu a gaban komai, tare kuma da kare tsaro da lafiyarsu.

A shekara ta 2020, cutar numfashi ta COVID-19 ta haifar da babban kalubale ga duk duniya. Kasa da kasa na ganin cewa, jam'iyyar kwaminis ta kaar Sin na jagorantar al'ummar kasar, wajen daukar kwararan matakan dakile annobar, inda aka maida moriyar al'ummar a gaban komai, da samun goyon-baya daga wajensu.

Kididdigar ta yi nuni da cewa, akwai 'yan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kusan miliyan 30, wadanda suka nuna himma da kwazo wajen yaki da cutar COVID-19, ciki har da guda 396 wadanda suka sadaukar da rayukansu, da guda 2337 wadanda suka harbu da cutar a yayin ayyukansu. Har wa yau, akwai mutane sama da dubu 25 wadanda suka zama 'yan jam'iyyar kwaminis a wuraren aikinsu na dakile yaduwar cutar a duk fadin kasar Sin.

Shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta tarayyar Rasha, Mista Gennady Zyuganov, ya yi tsokaci da cewa, a karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, jama'ar kasar sun samu muhimman nasarori wajen ganin bayan annobar. Har ma kasar Sin tana himmatuwa wajen taimakawa sauran kasashe yaki da cutar, al'amarin da ya shaida manufar raya al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

1  2  3  4  5  6  7  8  9  10  11  

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China