Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fashewar wasu tankokin ta yi sanadin mutuwar mutane akalla 4 a kudu maso yammacin Nijeriya
2020-06-22 10:12:26        cri
Mutane akalla 4 sun mutu, sanadiyyar fashewar wasu tankokin mai a kusa da birnin Lagos, cibiyar hada-hadar harkokin kasuwanci ta Nijeriya.

A cewar shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Lagos, Femi Oke Osanyintolu, fashewar tankoki na farko, ta faru ne da safiyar jiya Lahadi biyo bayan arangamar da tankoki biyu dake shake da mai suka yi a kan gadar Kara dake wajen birnin Lagos.

Baya ga tankokin biyu, gobarar da hatsarin ya haifar, ta shafi wata tanka ta daban da wata babbar motar dakon kaya, wanda ya yi sanadin fashewar tankar.

Hukumar kiyaye haddura ta kasar, ta bukaci direbobi su nemi wata hanya ta daban domin ba masu aikin ceto damar kammala aikinsu a kan gadar Kara. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China