Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 35
2020-05-25 10:37:13        cri

Kimanin mayakan kungiyar Boko Haram 35 aka kashe a yayin wasu hare haren kakkabe sansanonin 'yan ta'addan wanda sojojin Najeriya suka shafe kwanaki suna kaddamarwa a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

A wata sanarwa da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, rundunar sojojin ta ce, ta kaddamar da aikin kakkabe maboyar 'yan ta'addan ne tsakanin ranar 11 zuwa 22 ga watan Mayu inda ta yi nasarar kashe 'yan ta'addan masu yawa.

Babban hafsan sojojin Najeriyar Tukur Buratai, ya ce manufar kaddamar da hare haren na baya bayan shi ne domin murkushe 'yan ta'addan daga shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Tun a shekarar 2009, kungiyar Boko Haram take cigaba da yunkurin kafa daular musulunci a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, inda ta fadada kaddamar da hare harenta zuwa wasu kasashen dake tafkin Chadi.

Kungiyar ta haifar da gagarumar barazanar tsaro, da kalubaloli ga shirin bada jin kan bil adama da haifar da matsaloli ga gwamnatocin kasashen yankin tafkin Chadi, da suka hada da Najeriya, Chadi, Kamaru, Benin da Nijer, kamar yadda MDD ta ayyana.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China