Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundanr 'yan sandan Nijeriya ta tabbatar da kama mutane 799 bisa zargin aikata fyade
2020-06-16 10:45:54        cri
Sufeto Janar na 'yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, ya bayyana a jiya cewa, rundunarsa ta kama kimanin mutane 799 da ake zargi da aikata fyade a kasar, tsakanin watan Junairu zuwa Mayu.

Da yake ganawa da manema labarai a Abuja, Mohammed Adamu, ya ce dama ana samun matsalolin fyade da na cin zarafi, amma kuma matsalar ta yi kamari lokacin da ake kulle saboda COVID-19.

Ya ce tsakanin Junairu da Mayu, an bada rahoton fyade kimanin 717 a fadin kasar, yana mai cewa, 'yan sanda sun cafke mutane 799 da ake zargi da aikata laifin.

Ya ce a tsakanin lokacin, an gudanar da bincike tare da gabatar da laifukan fyade 631 a gaban kotu, yayin da ake ci gaba da bincike kan wasu 52.

Sufeto Janar din ya bukaci dukkan 'yan Nijeriya, su rika bada rahoton laifukan fyade ko wani nau'i na cin zarafi. Yana mai cewa, 'yan sanda za su ci gaba da daukan matakin da ya dace a kan kari.

A cewarsa, gwamnati za ta hada hannu da masu ruwa da tsaki a yankin yammacin Afrika, domin magance matsalar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China