2020-06-29 11:25:19 cri |
A cewar cibiyar nazarin kimiyya da injiniya ta jami'ar, jimillar wadanda suka kamu da cutar a fadin duniya ya karu zuwa 10,063,319
Cibiyar ta ce Amurka ce kasar da ta fi kowace masu yawan cutar, inda adadinsu ya kai 2,539,544 haka zalika wadanda suka mutu, inda adadinsu ya kai 125,747. Sauran kasashen da adadin wadanda cutar ta kashe ya zarce 20,000 sun hada da Brazil da Birtaniya da Italiya da Faransa da Spaniya da Mexico. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China