2020-06-19 11:36:59 cri |
Jami'ar ta nuna cewa, ana samar da a kalla sabbin riga kafin COVID-19 200, kuma kimanin 10 daga cikinsu sun shiga mataki na karshe na gwaji kan mutane, inda kuma guda 3 suka shiga mataki na uku na gwaji kan mutane, ciki har da na kasar Sin. Ta ce zuwa karshen shekara, akwai yiwuwar samun riga kafi 1 ko 2.
Ana fatan zuwa shekarar 2021, a samu riga kafi biliyan 2 da za a yi amfani da su a fadin duniya.
Soumya Swaminatan ta kara da cewa, WHO na shirya wani tsarin tantance wadanda za a fara ba riga kafin. Misali, wasu rukunonin jami'an dake gaba-gaba wajen yaki da cutar, da direbobi, da ma'aikatan motocin daukar marasa lafiya, da sauran ma'aikatan lafiya, da 'yan sanda, da ma'aikatan shaguna, da masu aikin tsafta, wadanda mai yiwuwa sun yi mu'amala da masu cutar. Amma abu na farko shi ne, bukatar bangarori daban daban su cimma matsaya. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China